Kungiyar Kiristocin Nijeriya CAN ta nuna goyon bayan ta kan hukuncin kisa da aka yanke wa wani matashi mai suna Yahaya Aminu Sharif da ya yi batanci ga Manzon Allah SAW a Kano.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Adeolu Samuel Adeyemo ya ce kungiyar ba ta da ta cewa tunda hukuncin ya yi dai-dai da tsarin musulunci.

Ya ce hukuncin kotun shari’ar musulunci yana da mihammanci don haka basu da wata hujja da za su soki hukuncin.

Adeyemo ya ce a cikin Kiristanci batanci ga Ruhu Mai Tsarki ba za a gafartawa wanda ya aikata haka ba.

Ya kara da cewa kutse a cikin hukuncin Musulunci bai dace ba ga duk wani kirista.

Idan za a iya tunawa, kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke hukunci kisa ga wanda ya yi batanci Manzon Allah.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *