Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, ta ce an samu nasarar ceto wani matashi da aka tsare a cikin gidan su tsawon shekaru bakwai ba tare da ba shi damar fita ba.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Haruna Kiyawa ya tabbatar wa manema labarai haka.

Da yammacin ranar Alhamis da ta gabata ne, bidiyon da ke nuna yadda aka kuɓutar da yaron ya watsu a shafukan sada zumunta, inda aka nuna yadda wasu mutane su ka ɗauke shi cikin motar ‘yan sanda aka tafi da shi, yayin da wasu mutanen ke tattaunawa da shi ya na nuna alamun farin ciki.
Lamarin dai ya na zuwa ne, daidai da ranar da ‘yan sanda su ka gurfanar da mahaifin yaron da aka ceto a Birnin Kebbi, bisa zargi matan uban sa da ɗaure shi a turken dabbobi tsawon shekaru biyu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *