Majalisar Shari’ar addinin Musulunci ta Nijeriya na cewa, gazawar gwamnatin tarayya wajen hukunta wadanda su ka janyo rikicin Zangon-Kataf ne abin da ya sababba rikicin jihar Kaduna.

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta yanke wa mutanen da aka samu da hannu a rikicin Zangon-Kataf shekaru 28 da su ka wuce hukuncin da ke kan su na kisan-kai.

Sakataren Majalisar AbdurRahman Hassan ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce dole a koma a duba abin da ya auku a lokacin gwamnatin soji.

Ya ce an samu wasu manya da laifin tada tarzoma a garin Zangon-Kataf da ke kudancin jihar Kaduna, amma shugaban kasa na wancan lokacin Janar Sani Abacha ya yi masu afuwa.

Malam AbdurRahman Hassan, ya ce majalisar ta na so a hukunta wadanda aka yi wa afuwa game da rikicin Zangon-Kataf, domin ta haka ne kawai za a samu zaman lafiya a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *