Hukumar ƙididdiga ta kasa, ta ce adadin rashin aiki ya kai kashi 27.1 a alƙalumman farko da ta fitar tun shekara ta 2018 a Nijeriya.

Adadin dai, ya ƙaru ne daga kashi 23.1 na rashin aikin yi da aka fitar a shekara ta 2018, zuwa kashi 27.1 a shekara ta 2020.

Hukumar, ta ce sama da kashi ɗaya bisa huɗu na ma’aikata sun rasa ayyukan yi a shekara ta 2020, kuma yawan adadin matasan da su ka rasa ayyukan yi tsakanin ‘yan shekaru 15 zuwa 34 ya kai kashi 34.1.

Annobar korona dai ta kara haifar da taɓarbarewar tattalin arziki a Nijeriya, bayan faduwar farashin danyen mai da cutar ta haifar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *