Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi, ta ce ta gurfanar da mahaifin yaron da aka ɗaure a turken dabbobi a gaban kuliya, bayan ta kammala bincike da ta ke yi a kan lamarin.

Ana dai tuhumar mahaifin ne da laifin tauye haƙƙin yaron, sakamakon gazawar mahaifin wajen sauke nauyin kula da ɗan da ya haifa.

A karshen makon jiya ne, jami’an wata ƙungiyar farar hula su ka bankaɗo inda aka ɗaure yaron, wanda daga nan ‘yan sanda da gwamnatin jihar Kebbi su ka shiga cikin maganar.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kebbi DSP Nafi’u Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa, mutumin ya tabbatar masu cewa an haifi yaron ne da wata rashin lafiyar taɓin hankali, saboda ya gaji da neman magani ne ya ɗaure shi don ya hana shi fita.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *