An samu gobara a wani rumbun ƙera makamai na rundunar sojin Sudan a yau Juma’a.

Lamarain ya faru ne a Khartoum babban birnin ƙasar.

Wasu shaidun gani da ido sun ce sun ji ƙarar fashewar abubuwa sa’annan suka ga wuta na tashi tare da hayaƙi mai kauri daga harabar wurin.

Wurin ƙera makaman dai na a gundumar Al-Shagara, kuma akwai wuraren ajiya na sojoji da dama a yankin.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta bayyana cewa tuni motar ɗaukar marasa lafiya ta isa wurin, amma babu wani rahoto na wasu da suka jikkata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *