Kasar Ireland ta sanya hannu kan yarjejeniyar maido wa da Najeriya Euro miliyan 5 da rabi daga cikin kudin da tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya ajiye a asusun bankin ajiyar kasar.

Ministar Shari’ar kasar Helen McEntee ta ce shirin maido wa Najeriya kudaden ya biyo bayan hukuncin kotu da ta bada umurnin yin haka a shekara ta 2015.

McEntee ta ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar ta rufe asusun ajiyar a shekarar 2014, bayan da wasu lauyoyi da aka tura daga Najeriya sun tuntubi gwamnatin Ireland.

Wannan sanarwa ta kawo karshen dogon lokacin da aka dauka wanda ya kunshi binciken kasashen duniya dangane da rufe asusun ajiyar tsohon shugaban kasar da ke kunshe da kudin da ya zarce sama da Dala biliyan guda, kuma Euro miliyan 5 da rabi na aje ne a kasar ta Ireland.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *