Jami’an tsaro sun samu nasarar kama wasu mutum 33 da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma sayar da kayayyakin da aka yi fasa ƙwaurin su a Arewacin kasar Kamaru da kuma wasu yankunan Adamawa da ke Najeriya.

Mai magana da yawun jami’an tsaron ya ce baya ga kama mutanen an kuma kwato babura da miyagun ƙwayoyi a wani shirin tsaro da sojojin ƙasar ke yi mai suna Adano.

Arewacin Kamaru dai ya yi ƙaurin suna wurin garkuwa da mutane inda aka fi kai wa makiyaya hari.

A 2018 kaɗai, akalla mutane 250 aka yi garkuwa da su a Adamawa da kuma Arewacin Kamaru.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *