Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce a ranar 31 ga Oktoba ne za a yi zabubbukan cike gurbi na mazabu 12 waɗanda su ka rage a dukkan fadin Nijeriya.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai na hukumar, Festus Okoye, ya fitar a Abuja.

Okoye ya ce in ba domin annobar korona da ake fama da ita ba, da tun tuni hukumar ta aiwatar da zabubbukan.

Za a gudanat da zabubbukan cike gurbin ne na ‘yan majalisun dattawa a jihohin Bayelsa, Cross River, Borno, Imo, Legas da Plateau.

Sauran jihohin sun hada da Zamfara da Kogi.

Okoye ya ce an yanke shawarar hakan ne bayan an gama duba tsare-tsaren da aka yi don gudanar da zabubbukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo da kuma sauran zaɓuɓɓukan cike gurbi.

Ya ƙara da cewa za a yi zabubbukan cike gurbin na majalisun tarayya da na jihohi ne a dalilin aje aiki ko mutuwa na membobin majalisun a jihohin takwas da abin ya shafa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *