Rundunar hadin gwiwa ta kasashe ta ce kungiyar Boko Haram ta fito da wasu sabbin dabaru na amfani da kananan yara a matsayin mayaka domin kara mata karfi a yankin tafkin Chadi.

Jami’in yada labarai na rundunar Kanar Timothy Antigha, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a N’Djamena, dake jamhuriyar Chadi.

Ya ce kungiyar ta’addancin nadaukar kananan yaran a matsayin mayaka ne sakamakon yadda mayakansu ke mika wuya, biyo bayan matsin lamba da suke fuskanta daga jami’an tsaro. 

Antigha ya ce sun sami wannan mummunan labari ne daga bayanan sirri da wasu daidaikun mutane da kungiyoyi ke basu a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Ya kara da cewa ita kanta kungiyar ta tabbatar da hakan a lokacin da ta fitar da wani bidiyon kananan yara na rike da manyan bindigogi da alburusai sanye da kayan soji.

Sannan ya gargadi matasa da suyi taka tsantsan da wasu dake musu alkawarin basu mulki, da kuma samar musu da kudade ta wata hanya ta daban.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *