Rundunar Sojin Sudan ta Kudu ta ce mutane 127 suka mutu sakamakon tashin hankalin da aka samu tsakanin wasu fararen hular dake dauke da makamai da sojoji.

Mai Magana da yawun sojin Manjo Janar Lul Ruai Koang ya ce rikicin ya barke ne ranar Asabar lokacin da ake kokarin karbe makamai daga hannun yan bindigar.

Janar Lul ya ce daga cikin mutane 127 da suka mutu, 45 jami’an tsaro ne, yayin da 82 matasa ne dake dauke da makamai.

Jami’in ya ce wasu sojoji 32 kuma sun jikkata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *