Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC na binciken wasu kan kasar Lebanon biyu kan zargin satar kudi naira milliyan dari 3 da 38.

Mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale, ya bayyana haka a cikin water sanarwa da hukumar ta fitar.

Ya ce hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya ce ta kama mutanen Dina Jihad da Chamseddine Wael Mohammed, a filin jirgin kasa na kada da kasa dake Fatakwal babban birnin jihar Rivers, inda ta hannan tasu ga EFCC.

A lokacin da yake mikasu ga hukumar, shugaban hukumar hana fasakwabri dake kula da shiyyar, Mohammad Olayinka, ya ce an kama mutanen biyu ne a lokacin da suke kokarin guduwa zuwa kasar su.

Ya ce an sanya kudaden da aka gano a wajen mutanen a asusun babban bankin Najeriya reshen jihar Rivers, bayan mutanen sun kasa kare kansu daga tambayoyin da aka rika musu akan kudaden.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *