Gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi sun ce akwai bukatar su maida hankali kan matasa ta yadda za su rika bada gudunmawa wajen dokoki da kuma harkokin gudanar da mulki.

Ministan kula da ayyuka na musamman Geoge Akume, ya bayyana haka a lokacin taron kwana guda na zagayowar ranar matasa da majalisar matasa ta Najeriya ta shirya a Abuja.

Ministan ya ce akwai bukatar matasa su rungumi harkokin noma, wanda hakan zai taimaka wajen rage zaman kashe wando a tsakanin al’ummar Najeriya.

Ya ce akwai shirye-shirye da dama da gwamnatin tarayya, da jihohi suka fito dasu na bada rancen kudade da kayyayyakin aikin gona, wanda a cewarsa anyi hakan ne domin inganta aikin noma.

A nasu jawabin wasu daga cikin gwamnonin jihohi, sun ce za su ci gaba da ba bangaren matasa muhimmanci, musamman wajen horas dasu kan sana’o’i daban-daban da kirkire-kirkire.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *