Majalisar zartaswa ta tarayya ta bukaci ma’aikatar kudi ta rika cirewa jihohin da ke cin tarar da bata kamata ba ga bangarorin hakar ma’adanai,  wasu kudade daga cikin kudaden da ake kasaftawa.

Ministan kula da harkokin yada labarai da al’adu Lai Muhammad, ya bayyanawa manema labaran fadar shugaban kasa haka jim kadan bayan kammala taron majalisar.

A cewarsa an dauki wannan mataki ne bayan wata wasika da ministan kuda da ma’adanai tama da karafa ya rubuta yana neman a amincewa ma’aikatarsa ta magance wasu matsaloli da bangaren ma’adanai ke fuskanta.

Muhammad ya ce kadan daga cikin matsalolin da ministan ya zayyano a wasikar sun hada da karbar haraji fiye da sau guda, matsalolin tsaro a wasu sassan kasar nan, da kuma katsalandan daga wasu masu ruwa da tsaki ciki har da sarakunan gargajiya.

Ya ce karbar haraji fiye da sau guda na korar wasu masu zuba jari da dama daga Najeriya.

Ya kara da cewa za a rika cire kudaden ne kai tsaye daga ma’aikatar kudi ga duk jiha, ko karamar hukumar da aka samu da aikata hakan ga bangaren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *