Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da bukatar cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC na kashe sama da naira billiyan 8 wajen sayo wasu na’urorin gwaje-gwajen cutar korona 12.

Ministan lafiya Osagie Ehanire, ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai na fadar shugaban kasa karin bayani bayan taron majalisar.

A cewarsa amincewar da majalisar ta yi zai taimakawa cibiyar ta NCDC samar da kayayyakin gwaji a dukkanin kananan hukumomi dari 7 da 74 dake fadin Najeriya.

Ministan ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa cewa kwamitin yaki da cutar korona da shugaba Buhari ya kafa ta yi watsi da kayayyakin gwaje-gwajen gaggawa da ake dasu.

Ehanire ya kuma nuna bacin ransa kan saba dokokin kariya daga cutar ta korona a wajen yakin neman zaben gwamnan jihar Edo da kuma wajen birne Buruji Kashamu a jihar Ogun.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *