Gwamnatin tarayya ta kwaso karin ‘yan Najeriya dari 2 da 92 daga Hadaddiyar Daular Larabawa Dubai, wanda hakan ya kawo adadin wadanda aka kwaso daga Dubai zuwa dubu 2 da dari 9 da 33.

Hukumar kula da ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen ketare NIDCOM ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na twitter.

A cikin sanarwar, hukumar ta ce mutanen da aka kwaso da jirgin kamfanin Emirates sun sun sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, dake Abuja.

Hukumar ta kara da cewa duk da gwaji ya nuna cikin mutanen ba mai dauke da cutar korona, za a killace sun a tsawon kwanaki 14, kamar yadda kwamitin yaki da cutar korona ya shawarta.

Ko a ranar Lahadin da ta gabata, hukumar ta sanar da maido da wasu ‘yan Najeriya dari 3 da 27 zuwa gida daga kasar Burtaniya, sakamakon kara tsaurara matakai da kasashen duniya ke yi na yaki da cutar korona.

Gwamnatin tarayya ta ce zuwa watan Yunin wannan shekarar, ta kashe naira milliyan dari da 69 wajen maido da ‘yan Najeriya gida daga kasashen ketare.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *