Hadaddiyar Daular Larabawa Dubai, da Kasar Isra’ila sun kulla yarjejeniyar diflomasiyya da ta kunshi zaman lafiya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da shugaban kasar Amurka Donald Trump da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Yarima mai jiran gado Mohammed Al Mahyan suka fitar.

Sanarwar ta ce wannan mataki na ci gaba da kasashen suka dauka zai taimaka wajen kawo zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Sun kuma bayyana cewa hakan na nufin Isra’ila za ta dakatar da yunƙurin da take yi na mamaye wani yankin gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Har yanzu dai, Isra’ila ba ta da wata alaƙa ta diflomasiyya da ƙasashen Larabawa da ke yankin Gulf.

Wannan yarjejeniyar da aka cimma ita ce ta uku tsakanin Isra’ila da ƙasashen Larabawa tun bayan samun ‘yancin kai na Isra’ila a 1948.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *