Mutane 4 sun rasa rayukansu rikicin da biyo bayan bayan zanga zangar adawa da takarar shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara wanda ke neman wa’adi na 3 a zaben shugaban kasar da zai gudana a watan Oktoba.

Wasu majiyoyi sun ce an kashe mutane 3 a tsakiyar birnin Daoukro lokacin da aka fafata tsakanin magoya bayan Ouattara da masu goyan bayan abokin adawar sa Henri Konan Bedie.

Haka kuma a yau Alhamis jami’an tsaro sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a garin Banoua lokacin da akayi fito na fito da jami’an tsaron.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun mamaye tashar Yan Sandan Banoua, abinda ya tilastawa jami’an su neman mafaka, kamar yadda wani mazaunin garin Herve Niamkey ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Ouattara mai shekaru 78 ya bayyana aniyar sa ta sake takara a makon jiya, bayan mutuwar Firaministan sa kuma dan takarar Jam’iyar su Amadou Gon Coulibaly.

Ya zuwa yanzu Jam’iyyar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo FPI bata bayyana wanda zai tsaya mata takara ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *