Darikar Tijjaniyya ta nesanta kanta da matashin da Kotun Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa a Kano Yahaya Sharif Aminu, bayan ta same shi da laifin yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW.

Shugaban majalisar zawiyoyin Tijjani a Kano, Muhammad Nura Arzai ya ce ko kaɗan abin da matashin ya aikata ba ya cikin ladubba da koyarwar Sheikh Ibrahim Inyas.

Karon farko kenan da ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin addini ta mayar da martani kan hukuncin da aka yanke wa matashin mai shekaru 22 ranar Litinin.

A ranar Litinin ne kotun da ke zamanta a unguwar Hausawa a birnin Kano ta ce za a rataye Yahaya Aminu har, sai dai ta ce yana da damar daukaka kara.

Tun a watan Maris na 2020 Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa mai dauke da batanci.

Haka zalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *