Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya ta ba `yan Najeriya da suka mallaki hankalin kansu lasisin mallakar bindiga samfurin AK47 domin su kare kawunansu daga ‘yan ta’adda.

Ortom ya yi wannan bayanin ne a cikin wata kasidar da ya gabatar a wani taron gwamnonin Najeriya da aka yi ta fasahar zamani.

Ya ce hakan shine mafita domin manyan makaman da ke hannun miyagu sun fi karfin bindigar da doka ta ba da izinin mallaka.

Ya kara da cewa jami`an tsaron Najeriya na iya bakin kokarinsu, sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba, bisa la`kari da hare-haren da `yan boko haram da `yan bindiga masu satar mutane ke kai wa a wasu sassan kasar nan.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *