Kotun Shari’ar Musulunci da ke jihar Kano ta yankewa wani tsohon hukuncin kisa sakamakon kamashi da laifin yiwa wata yarinya FYADE.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki, ya ce za a kashe mutumin ne mai shekaru 70, ta hanyar rajamu.

Kotun ta samu mutumin, wanda dan karamar hukumar Tsanyawa ne, da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyade.

Mutumin ya amsa laifin da ake tuhumarsa akai, kuma sau hudu ana dage shari’ar domin alkali ya ba shi dama ko zai sauya matsayinsa, sai dai duk lokacin da aka koma kotu yana jaddada mata cewa shi ne ya yi wa yarinyar fyade.

Duk da mutumin ya nemi tafiya, sai dai alkali Ibrahim Sarki ya karanto sassan Al-Kur’ani mai tsarki da kuma wasu hadisai wadanda suka nuna girman laifin da ya aikata.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *