Gwamnatin tarayya ta amince da a kwaso rukunin karshe na ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Amurka, tun bayan bullar cutar Korona a kasashen duniya.

Jakadan Najeriya a kasar Amurka Benaoyagha Okoyen, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a New York a madadin ofishin jakadancin Najeriya.  

A cewarsa akwai jirgin karshe da aka kammala shirye-shiryen tasowarsa daga New Jarsey a ranar 20 ga watan Augustan nan da muke ciki zuwa filayen jiragen sama na Abuja da Legas.

A cewarsa wannan zai zo ne bayan wadanda aka shirya tasowarsu a ranakun 15 da 19 a watan na Augusta a daga Houston da Texas zuwa Legas.

Kawo yanzu dai gwamnatin tarayya ta kwaso mutane dubu 1 da dari 7 da 39 da suka makale a kasar ta Amurka tun bayan bullar cutar tare da daukar matakan rufe kan iyakokin kasashe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *