Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kara rawar gani a yaki da take da ayyukan ta’addancin Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban shawara na musamman akan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Femi Adesina ya fitar a Abuja.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da gwamnonin yankin yayin ziyarar da suka kai masa a fadarsa dake Abuja.

Ya kara da cewa gwamnatinsa na iya bakin kokarin ta wajen ganin ta magance matsalar tsaro, amma hakan na samun tsaiko ne sakamakon karancin isassun kayayyakin aiki da jami’an tsaro.

A nasa jawabin shugaban gwamnonin yankin wanda shine gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce samar da yanayi mai kyau ga mutane ta yadda za su koma gidajensu da gonaki zai taimaka wajen rage ayyukan ta’addancin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *