Ministan kimiyya da fasaha Ogbonnnaya Onu, ya bukaci cibiyoyi dake karkashin ma’aikatarsa su ci gaba da binciko hanyoyin da za su kawo ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Onu ya bayyana hakan ne a taron wata hurhudu da ake gudanarwa a tsakanin masu ruwa da tsaki da shugabannin bangarori na hukumar a Abuja.

Ya ce cigaba da karin binciken ze taimaka wajen kara samar da kudaden shiga ta bangaren da kuma kara bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi tsakanin al’umma.

A cewar ministan yawaita binciken zai kara ba matasa kwarin gwiwa na kara bada gudunmuwa ta hanyan bayyana fasahar da suke da ita da zasu iya amfanar kasa baki daya.

A nasa jawabin karamin minstan ma’aikatar Muhammad Abdullahi, ya shawarci hukumomin su cigaba da aiki kafada da kafada domin samar da cigaban da ake bukata a bangaren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *