Jami’an tsaro sun kama mutane takwas da ake zargi da hannu a kashe-kashen baya-bayan nan a kudancin jihar Kaduna.

Shugaban runduna ta musamman dake yaki da ayyukan ta’addanci a yankin da ake yiwa lakabi da Operation Safe Haven Kanar David Nwankonobi, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kafanchan.

Ya ce an kama mutanen ne a Unguwanni biyu biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan irin shirye-shirye da kuma hare-haren da suka kai a baya.

Wannan na zuwa ne bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai, inda suka kashe mutane 30 tare da raunata wasu da dama, baya ga asarar dukiyoyi da ka yi.

Ya kara da cewa makaman da aka kama a hannun mutanen sun hada da bindgogi ƙirar hannu da gatari masu yawa da kuma babura.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *