Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatar da matakin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dauka na kwace rijistar jam’iyyun siyasa 22.

A lokacin da yake yanke hukuncin, mai shari’a Monica Dongban Mensem, ta ce hukumar zabe ta yi watsi da wasu ka’idoji a sashe na 225 na kundin tsarin mulki.

Ta ce banda cewa maganar na gaban kotu, hukumar ta yi gaban kanta wajen soke rijistar jam’iyyun ba tare da sanar dasu irin sharuddan da basu cika ba.

Jam’iyyun dai na daga cikin jam’iyyu 74 da hukumar zaben ta soke rijistarsu a watan Fabrairun wannan shekarar sakamakon rashin cika ka’idojin da kundin zabe ya tanada.

Kotun ta ce sashe na 40 na kundin tsarin mulki ya ba duk wani dan kasa damar kafa kungiya, kuma hakan ya kunshi jam’iyyun siyasa a duk lokacin da suke so.

Sai dai a nata bangaren hukumar zaben ta sha alwashin daukaka kara zuwa kotun koli kan hukunci da kotun daukaka karan ta yanke.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *