Gwamnatin tarayya ta jaddada goyon bayan ta ga kokarin da kasashen kungiyar rainon tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ke yi wajen amfani da shirin sauya yadda ake gudanar da rayuwa da kungiyar ta fito da shi.

Ministan kula da harkokin muhalli Mahmood Abubakar ya bayyana haka a lokacin taron kwanaki biyu ta fasahar zamani da kasashen ECOWAS 15 suka halarta.

Abubakar ya ce gwamnatin tarayya za ta bada dukkanin gudunmawar da ake bukata tare da dukkanin shawarwarin da aka amince dasu kan sake sauya yadda ake tafiyar da rayuwar yau da kullum.

Ya ce ma’aikatar kula da muhalli za ta ci gaba da aiki da sauran wadanda suka fito da tsare-tsaren dan tabbatar da an samu ci gaba irin na kasashen duniya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *