Babban jami’in kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kan yaki da cutar Korona Sani Aliyu, ya ce yawan wadanda ake samu da cutar korona na raguwa.

Aliyu wanda ya bayyana hakan ne a wajen taron kwana-kwana da kwamitin ke shiryawa a Abuja, ya ce hakan ba shi ke nuna cewa anyi nasarar yakar cutar ba.

Ya ce ya zama wajibi a ci gaba da bin ka’idojin kariya daga cutar dan tabbatar da cewa an ci gaba da rage yawan wadanda sutar ke kamawa kullum a Najeriya.

A nasa jawabin ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire, ya ce a yanzu gwamnatin tarayya ta fi maida hankali kan yadda za ta rage yawan masu mutuwa sakamakon kamuwa da cutar da kasa da kashi 1 cikin dari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *