Gwamnatin jihar Kogi ta nuna gamsuwarta da ka’idojin kariya daga cutar korona da makarantun jihar suka dauka, bayan sake bude su bisa umurnin gwamnatin tarayya.

Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasa na jihar Wmi Jones, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan ya kai ziyarar gani da ido a wasu kamarantun jihar.

Kwamishinan ya yabawa shugabanni da malaman makarantun bisa tsayin daka da suka yid an tabbatar da ganin anbi ka’idojin da ake bukata na kariya daga cutar.

A lokacin da yake yiwa daliban jawabi, kwamishinan ya yiwa daliban maraba da dawowa karatu, tare da bayyana musu cewa gwamnatin jihar ta yi iya bakin kokarin ta na ganin sun koma makaranta.

Sannan ya shawarci daliban da su kula da kawunansu, musamman wajen kasancewa a cikin tsafta kowawane lokaci, tare da bin matakan kariya daga cutar.

Ya kuma bukaci daliban da su ci gaba da amfani da tsarin da aka fito dashi ta yanar gizo na karatu kan jarabawar kammala makarantar sakandire ta yammacin Afrika WAEC.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *