Gwamnatin jihar Kano ta ce ta samar da karin sabbin makarantun tsangayu na zamani 3 domin inganta harkokin almajirai dari 9 da 76 da aka maida jihar daga wasu jihohi.

Shugaban hukumar kula da harkokin karatun Al-Kur’ani da addinin Musulunci na jihar Gwani Yahuza ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Yahuza ya ce an samar da makarantun ne a matsayin kari kan tsangayu 12 da ake dasu a fadin jihar domin koyar da yaran ilimin addini, karatun Al-Kur’ani da kuma na zamani.

A cewarsa ko wani makaranta a cikin makarantun zai dauki dalibai dari 3, wanda an samar da kayayyakin karatu da kuma na inganta rayuwa da yanayi mai kyau ga malaman da kuma dalibai.

Yahuza ya ce hukumar da yake jagoranta na aikin sanya ido ne kan makarantun domin tabbatar da ana aikata abin da ya kamata a bangaren.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *