Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da gwamnonin yankin arewa maso gabashin Nijeriya da manyan hafsoshin soji a fadar sa da ke Abuja.

Daga cikin gwamnonin da su ka halarci ganawar, akwai Borno Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno, da Amadu Umar Fintiri na jihar Adamawa, da Bala Mohammed na jihar Bauchi da kuma Inuwa Yahaya na jihar Gombe.

Sauran sun hada da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, da mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Janar Babagana Monguno, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da Janar Tukur Yusuf Buratai, da Janar Abayomi Olonisakin, da ministan kula da harkokin ‘yan sanda Muhammad Dingyadi.

Bayan ganawar, Gwamna Zulum ya shaida wa manema labarai cewa, sun tattauna ne a kan muhimman ƙalubalen da yankin ya ke fama da su, musamman matsalar tsaro da taɓarɓarewar abubuwan more rayuwa da kuma batun haƙo man fetir a yankin.

An dai yi ganawar ne, bayan zargin zagon ƙasa da gwamna Zulum ya yi wa rundunar sojin Nijeriya saboda harin da ‘yan Boko Haram su ka kai wa tawagar sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *