Kungiyar kare hakkin musulmai ta Nijeriya MURIC, ta zargi gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishaku da maida Musulman jihar saniyar ware.

MURIC ta ce gwamnatin Ishaku ta dauki Kiristocin jihar da Jukunawa a matsayin ‘yan lele wajen raba masu duk wata dama da aka samu.

Shugaban kungiyar na kasa Farfesa Ishaq Akintola ya bayyana wa manema labarai haka, inda ya ce wajibi ne su binciki ayyukan gwamnan, musamman a kan yadda ya ke danne musulmai da ba kabilar Jukkunawa ba.

Akintola ya kara da cewa, a karkashin jagorancin Darius Ishaku, an kiristantar da duk wasu bangarorin gwamnati, musamman a kan bubuwa da su ka shafi harkokin ilimi da daukar aiki da kuma rabon mukaman siyasa.
Kungiyar, ta ce shekaru biyar kenan ana fama da yi wa musulmai makirci da nuna masu kiyayya a lokacin  shiga makarantun gaba da sakandare, inda ake ware damar karatu kyauta, amma ana fifita Kiristoci da Jukkunawa da sauran kabilu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *