Wata babbar kotun Shari’a da ke birnin Kano, ta zartar da hukuncin kisa a kan wani matashi mai suna Yahaya Aminu Sharif, saboda wallafa wata wakar batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.).

Wata majiya ta ce alkalin kotun mai shari’a Khadi Aliyu Muhammad ne ya zartar da hukuci.

Majiyar ta ce, alkalin ya zartar da hukuncin ne bayan ya gamsu da hujjojin cewa, matashin ya aikata laifin da ya janyo aka gurfanar da shi a gaban kotu.

An dai gurfanar da matashin mawaki a gaban kotu ne, bayan an zarge shi da wallafa wata waka mai dauke da kalaman batanci ga Annabi Muhammad (S.A.W.) a cikin watan Maris na shekara ta 2020.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *