Gwamnonin yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, sun bukaci gwamnatin tarayya ta kwace aikin Tituna daga ‘yan kwangilar da su ka kasa ci-gaba da ayyukan su, domin a ba wadanda za su iya aikin cikin takaitaccen lokaci.

Kungiyar ta yi kiran ne, a wani taron gwamnonin da su ka gudanar a garin Maiguduri, wanda ya samu halartar Gwamnonin jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Gombe da Taraba da kuma Yobe.

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ne ya jagoranci taron, inda ya ce sun yaba wa gwamnatin tarayya tare da rundunar sojin Nijeriya bisa yakin da su ke yi da kungiyar Boko Haram.

Sai dai gwamnonin sun yi kira ga sojojin su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula.

Gwamnonin, sun kuma yi alkawarin hada kai da gwamnatin tarayya wajen habbaka makarantun tsangaya da karfafa karatun Islamiyya da na zamani da kuma hana yawon barace-barace.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *