Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, ya ce a halin yanzu ba ya da wani buri na barin jam’iyyar PDP ya koma tsohuwar jam’iyyar sa APC.

Ortom ya bayyana haka ne, a wajen taron jam’iyyar APC na zaben kwamitin shugabancin jam’iyyar a jihar, inda mulki ya cigaba da zama a hannun John Ngbede.

Gwamna Ortom, ya ce jam’iyyar APC ta aika ma shi goron gayyatar komawa cikin ta amma bai karba ba, ya na mai cewa zai cigaba da zama a jam’iyyar PDP.

Haka kuma, wakilan zaben sun nuna gamsuwar su a kan yadda Ortom yak i komawa jam’iyyar APC.

Yanzu haka dai da an  warware matsalar sabanin da ake samu na karba-karbar shugabanci a jihar, inda ake zargin kabilar Tiv ce ke mulki tun a shekara ta 1976.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *