Dan wasan shirin kwana chasa’in mai suna Sahir Abdul’aziz Wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin kwana chasa’in da ake gabatarwa a Arewa24 Ya rabu da Amaryar sa Wanda aka daura masu aure a watan afrilun wannnan shekarar.

Tun farko dai auren nasu ya janyo hankulan mutane sosai musamman ganin yadda ya auri wacce ake ganin ta girme shi, inda mutane ke ta tsokaci kala kala. Amman a lokacin malam Ali yace soyayya ce ta sashi auren honorabiyar inda har yaba matasa ‘yan uwansa shawara akan su dinga auren wanda suka girme su domin sunna ce mai karfi daga fiyayyen halitta.

Sai dai matasa a lokacin sun fito da wata kalma na” WUFF” musamman a kafafen sada zumunta na zamani, Inda suke fadin anyi wuf ne da Ali. Kuma suma indai hajiya ce mai naira zasu yarda ayi wuff dasu yayin da wasu ke ganin hakan Sam bai dace ba.

Sai dai kwatsam yau lahadi muka samu labarin rabuwar auren inda majiyarmu ta yi iya bakin kokarin ta domin jin musabbabin rabuwar auren amma hakan yaci tura.

Ra’ayoyi 2

Your email address will not be published. Required fields are marked *