Kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin Nijeriya, ta bukaci gwamnatin tarayya ta kara azama wajen yaki da kungiyar Boko Haram a yankin.

Gwamnonin sun yi kiran ne, yayin wanin kungiyar da ya gudana a Maiduguri.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Borno Isah Gusau, ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnonin sun cimma matsaya a kan batutuwa da dama, ciki har da bukatar gwamnatin shugaba Buhari ta sama wa sojojin da ke yaki da ayyukan ta’addanci a yankin karin makamai na zamani.

Gwamnonin, sun kuma a sama wa ‘yan sanda makamai na zamani domin taimaka wa sojoji wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Ya ce ko da ya ke gwamnonin sun yaba wa kokarin gwamnatin tarayya game da matakan da ta ke dauka ta fuskar yaki da ta’addanci, sai dai sun ce akwai bukatar ta sake tashi tsaye domin kawo karshen matsalar.
Haka kuma, sun zabi gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a matsayin shugaban kungiyar da zai jagorance ta har nan da tsawon shekaru biyu masu zuwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *