Hukumar kula da sufurin jiragen ƙasa ta Nijeriya NRC, ta ce ta samu kuɗin shiga sama da naira biliyan 3 a shekara ta 2019 ta hanyar zirga-zirgar jiragen a faɗin Nijeriya.

Babban daraktan hukumar Mista Fidet Okhiria ya bayyana haka a madadin minsitan sufuri, inda ya ce sun samu naira biliyan 1 da rabi ne daga jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce jirgin Abuja zuwa Kaduna ya na samar da kusan naira miliyan 130 duk wata a shekara ta 2019, saɓanin naira miliyan 80 da aka riƙa samu a shekara ta 2018.

Okhiria Ya ƙara da cewa, kuɗin da aka samu daga jirgin Kaduna an yi amfani da su ne wajen gina sauran tashoshin jirgin ƙasa a yankin Arewa.

Ya ce a gefe guda kuma, ɓarkewar annobar korona a Nijeriya za ta shafi hasashen kuɗin da ya kamata a samu na shekara ta 2020.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *