Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya ce jam’iyyar PDP ce za ta lashe zaben shekara ta 2023.

A wata hira da gwamnan ya yi da manema labarai, ya ce kawunan ‘yan jam’iyyar APC a rarrabe su ke, kawai sun hadu ne ta bangaren shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce sun san jam’iyyar APC gamin-gambiza ce, na mutanen da  su ka hada kawunan su daga wurare daban-daban, amma har yanzu kawunan su a rarrabe su ke.

Gwamnan ya cigaba da dewa, ‘yan Nijeriya sun gani a kasa, kuma sun san cewa jiki magayi, domin baya ga yunwa da wahala kasuwanci duk ya karye.

Ya ce da izinin Allah mutanen Nijeriya idon su ya bude, kuma rana ya fito duhu ya yaye.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *