Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya gargadi ‘yan siyasa su kauce wa duk wani yunkurin da zai haifar da tashin hankali, yayin da ya bukaci su rungumi hanyar inganta zaman lafiya da ci-gaban kasa.

Da ya ke jawabi a wajen taron shugabannin ‘yan kabilar sa ta Ijaw, Jonathan ya ce ya zama wajibi ‘yan siyasa su sa ci-gaban kasa a gaba, domin abin da siyasa ke bukata kenan ba raba kawunan jama’a ko kuma yaki da abokan gaba ba.

Yace a matsayin sa na mai fafutukar ganin dimokiradiya da shugabanci nagari ya wanzu a Nijeriya da Afirka, bukatar sa ita ce ganin jama’ar sa sun taka gagarumar rawa wajen zaben wanda zai jagorance su da kuma yadda ake jagorancin.

Jonathan ya kara da cewa, babu abin da ke maida al’umma ko kasa baya da ya wuce tashin hankali da kuma rikicin shugabanci, ya na mai cewa babu yadda za su yi ikrarin son jama’ar su a daidai lokacin da su ke amfani da damar domin cimma biyan bukatun kan su.
A karshe ya ya bukaci hadin kan jama’ar Nijeriya, da kuma kaunar juna wajen kulla kawance daga kowane sashe domin fuskantar kalubalen da su ka addabi jama’a a wannan lokaci.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *