‘Yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje 87 ne su ka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja.

Hukumomin Nijeriya dai sun kwaso mutanen ne daga kasar Sudan bayan, sun maƙale a can sakamakon dokokin kulle da annobar korona ta haddasa.

Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ketare NIDCOM, ta ce jirgin su ya sauka da misalin ƙarfe 09:15 na safe, kuma za su killace kan su na tsawon mako biyu masu zuwa.

Haka kuma, ta ce akwai wasu ‘yan Nijeriyar da za su dawo daga birnin London na kasar Birtaniya, inda ake sa ran saukar su a birnin Abuja.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *