Tawagar Gwamnatin Nijeriya a ƙarkashin jagorancin Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ta isa kasar Senegal, domin ta’aziyyar rasuwar jagoran Ɗariƙar Tijjaniya a Afrika Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass.

A cikin wani saƙo da mai ba shugaban ƙasa shawara a kan kafofin yada labarai na zamani Bashir Ahmed ya wallafa a shafin sa na Twitter, ya ce daga cikin waɗanda su ka je Senegal amadadin Shugaba Buhari akwai Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya Muhammed Babandede.

Idan dai ba a manta ba, a wannan makon ne Marigayi Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass ya riga mu gidan gaskiya, kuma tuni an yi jana’izar sa a birnin Kaulaha da ke ƙasar Senegal.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *