Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya, ya bayyana damuwa game da taɓaɓarewar siyasar Jihar Edo, wadda hukumar zabe ke shirin gudanar da zaɓen gwamna a watan Satumba.

A cikin wata sanarwa da ofishin jakadancin ta ya wallafa a shain sa na Twitter, Amurka ta ce ba ta ji daɗin abubuwan da ‘yan siyasa a jihar Edo ke aikatawa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Amurka za ta tallafa wa Nijeriya wajen tabbatar da dimokraɗiyya matuƙar za a riƙa ba talakawan Nijeriya waɗanda su ka zaɓa.

Jijiyoyin wuya dai sun fara tashi ne a Jihar Edo, bayan rantsar da ‘yan majalisar dokoki na jihar su 14 da su ka yi yunƙurin karɓe ikon majalisar.

Amurka, ta ce ta na kallon Nijeriya a matsayin uwa a Afirka, sannan ta yi kira ga masu ruwa da tsaki ciki har da hukumar zaɓe su tabbatar an yi zaɓen adalci kuma mai cike da zaman lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *