Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba ya son tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a zaben shekara ta 2023.

El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta BBC, inda ya ce ya kamata mulki ya koma kudancin Nijeriya a shekara ta 2023 bayan wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya kare.

Ya ce ana cewa ya na son shugabancin Nijeriya tun  ya na ministan Abuja, lamarin da ya bayyana a matsayin shirme.

Gwamna El-Rufa’i, ya ce Allah shi ya ke ba da mulki, kuma ko ka na so ko ba ka so idan ya na so zai ba ka, amma ya ce shi ban taba neman shugabancin Nijeriya ba.

Ya ce a siyasar da ake yi a Nijeriya akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince da cewa idan arewa ta yi mulki shekaru takwas, yankin kudanci ma zai yi mulki tsawon shekaru takwas, kuma duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓa a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a Nijeriya ya san da shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *