Bankin Duniya ya amince ya ba Nijeriya tallafin dala miliyan 114 da 28, kwatankwacin naira biliyan 43 domin yaƙi da annobar korona musamman a matakin jihohi.

A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce dala miliyan 100 za ta fito ne daga ƙungiyar tabbatar da ci-gaba da kasa da kasa IDA, sai kuma dala miliyan 14 da 28 da za su fito daga sashen bada agajin gaugawa, wato Pandemic Emergency Financing Facility a Turance.

Ta ce Gwamnatin Nijeriya za ta ba jihohi 36 lamuni ciki har da Abuja, ta hanyar tsarin yaƙi da annobar da aka yi wa laƙabi da COVID-19.

Sanarwar ta ƙara da cewa, shirin zai taimaka matuƙa a matsayin ɗaukin gaugawa da zai daƙile bazuwar cutar a tsakanin al’umma.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *