Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa a kan zarge-zargen da ake yi wa dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, ya ce zai tabbatar da ganin ya saurari Ibrahim Magu.

Yayin zaman ci-gaba da sauraren bahasi game da binciken, wata majiya daga kwamitin ta shaida wa manema labarai cewa, kwamitin ya ki amincewa a dauki hoton bidiyo, amma an tabbatar wa Magu cewa za a saurare shi.

Kwamitin ya ce shi ke da alhakin bincike, don haka bukatar Magu ta cewa a dauki zaman a hoton bidiyo ba zai yiwu ba, domin kwamitin bai san amfanin da za a yi da shi ba.

Majiyar ta cigaba da cewa, Kwamitin ya dauki alkawarin sauraren Ibrahim Magu da duk abubuwan da zai gabatar.
An dai kama Ibrahim Magu ne tare da tsare shi a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli na shekara ta 2020, bayan wani kiran gaugawa da kwamitin fadar shugaban kasa ya yi ma shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *