A ranar juma’a 7 ga agusta na shekarar 2020 ne aka yi jana’izar dan jarida Ladan Ibrahim Ayawa da ya riga mu gidan gaskiya ranar laraba 5 ga watan agustar nan.

Marigayi Ladan Ibrahim Ayawa

Idan an tuna mun bada rahoton rasuwarsa a wannan kafa. Ladan dadadden ma’aikacin radiyo ne da ya shafe shekaru yana aiki a Radio Najeria har zuwa ritayarsa a wajen. Bayan nan ne kuma ya fara aiki da Murya Amurka a matsayin wakilinsu na Legas kafin daga bisani suka dauko shi aiki na dindindin a shelkwatar Muryar Amurka da ke birnin Washington DC.

Mahalarta jana’izar Marigayi Ladan Ayawa

Kafin ajiye aikinsa na Muryar Amurka, Ladan yana daga cikin masu gabatar da labarai da shirye-shiryen radiyo irin su Himma Bata Ga Raggo da sauransu. 

Daya daga ‘ya’yan Ladan ne nan a tsakiya da kaya ruwan kasa a wajen jana’izar.

‘Yan uwa da abokan arziki sun taru an masa jana’iza tare da binne shi a makabartar kungiyar musulmin Amurka (All Muslim Association of America) da ke garin Fredericksburg a karamar hukumar Spotsylvania ta jihar Virginia a Amurka.

Jama’a na addu’a a gaban kabarin Marigayi Ladan Ibrahim


Bayan binne shi an gabatar da addu’o’i tare da jajantawa juna wannan babban rashi. Daga cikin wadanda suka halarta har da membobin kungiyar Hausawan Amurka ta Dangi Forum da kuma tsoffin abokan aikinsa na Muryar Amurka karkashin jagorancin shugabansu Aliyu Mustapha Sokoto. Allah ya ji kan Ladan, mu kuma ya kyautata karshenmu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *