A kalla mutane 20 ne su ka rasa rayukan su, yayin da wasu da dama su ka jikatta sakamakon sabbin hare-haren da aka kai a wasu garuruwa uku da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce ana zargin ‘yan daba ne su ka kai harin a ranar Alhamis din nan.

Garuruwan da aka kai harin sun hada da Kurmin Masara da Apyia Shyim da kumaTakmawai.

Sabon hari ya na zuwa ne, kwanaki kadan bayan an tura jami’an tsaro zuwa wasu garruruwan da ake ganin su na cikin hatsari ko kuma rikici ya na iya barkewa.

Rundunar ‘yan sanda ba ta tabbatar da harin ba, amma shugaban karamar hukumar Zangon Kataf Elias Manza ya shaida wa manema labarai cewa, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a garuruwan uku da asubahin ranar Alhamis din nan su na harbe-harbe.
Ya ce an kashe mutane bakwai a Takmawai, yayin da aka kashe wasu 13 a Kurmin Masara, sannan sun kone gidaje da dama yayin da mazauna garin su ka yi hijira zuwa kauyukan da ke makwabtaka da su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *