Wani matashi mai suna Abdullahi Bashir mai kimanin shekaru 25 zuwa 26 a jihar Adamawa, ya fada soyayya da Hanan Buhari yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Matashi Abdullahi Bashir ya kwashe kusan wata guda a garin Abuja ko Allah zai taimaka masa ya hadu da Hanan Buhari amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Hakan ya tilasta masa komawa ta kafafe sada zumunta domin isar da sakon soyayyarsa ga Hanan.

Ko da Radio Talaka ta tambayi Abdullahi Bashir ko me dalilinsa na fadawa soyayya da Hanan Buhari?

Matashin ya ce shi tunda yake a duniya bai taba soyayya ba, amma rana daya da yaga Hanan tana daukan hoton a gun taro sai yaji ta kwanta masa a zuciya, kuma ya sha alwashin sai ya aure ta.

Abdullahi dai yanzu ya sha alwashin bada shanaye 150 a matsayin sadaki indai har Hanan ta amince da soyayyarsa.

Ya kara da cewa duk dacewa shi ba mai kudi bane kuma ba dan mai kudi bane amma ya tabbata shanu 150 zai bayar a masayin sadakin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *