Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na 3 ya bukaci shugabanni su rika daukar shawarwari a koda yaushe tare da yin gyara a lokacin da suke kan karagar mulki.

Basaraken ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi yayin da suka kai masa gaisuwar ban girma.

Sultan ya bukaci shugabanni da su ji tsoron Allah, duba da cewa akwai ranar da za su kare kawunansu a gaban Allah Madaukakin Sarki kan irin jagorancin da suka yi.

Sarkin ya kuma bukaci al’ummomin Kano da su rungumi canje-canje da aka samu a Masarautar jihar, tare da yiwa sabbin shugabannin addu’ar samun ci gaba.

Ya kuma bukaci ‘yan majalisun sarakuna su rika fadawa sarakunan gaskiya tare da janyo hankalinsu a duk lokacin da suka ga za su yi kuskure.

Da yake magana sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya ce sun kai ziyarar ce domin jaddada mubaya’ar da suke da ita ga Masarautar Musulmi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *